An kai samame a Samsung kan zargin cin hanci a Korea ta Kudu

Samsung Korea ta Kudu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Samame a ofisoshin kamfanin Samsung kan zargin cin hanci

Masu gabatar da kara na kasar Korea ta Kudu sun kai samame a ofisoshin kayan lataroni na kamfanin Samsung.

Masu gabatar da kara na kasar Korea ta Kudu sun kai samame a ofisoshin kayan lataroni na kamfanin Samsung, a wani bangare na bincike kan badakalar siyasar da ta shafi shugaba Park Geun-hye.

Masu gabatar da karar na gudanar da bincike kan zargin cewa kamfanin na Samsung ya bai wa 'yar Choi Soon-sil, aminiyar shugabar kasar wasu kudade.

An zargi Ms Choi da amfani da abokantakar wajen yin katsalandan a cikin siyasar kasar da neman alfarmar kasuwaci.

Kamfanin na Samsung ya tabbatarwa da BBC samamen, amma ya ce babu wani karin bayani da zai kara yi a kai.

Shugaba Park ta nemi gafara kan alakar ta da Ms Choi, amma tana fuskantar matsin lambar ta yi murabus.

Cikin kwanaki kadan da suka gabata, dubban mutane a Korea ta Kudun sun yi ta zanga-zanga a Seoul babban birnin kasar, suna kira ga shugaba Park ta yi murabus kan badakalar cin hanci.

Ms Choi, wacce daddiyar aminiyar Ms Park ce, diyar wani shahararen jagoran addinin gargajiya ne Choi Tae-min, da ke da alakar kud- da-kud da mahaifin Ms Park, kana ita kan ta shugaba Park Chung-hee.

Ms Park ta kasance shugabar kasa ta farko mace, lokacin da aka zabe ta a zaben da aka gudanar a shekara ta 2012.