China : Ana kokarin ceto yaron da ya fada rijiya.

Asalin hoton, The Paper
Masu aikin ceto sun shafe kwanaki suna kokarin zakulo yaron da ya fada busasshiyar rijiya
Masu aikin ceto a kasar China sun shafe kwanaki suna kokarin zakulo karamin yaron da ya fada cikin wata tsohuwar rijiya.
Tun a ranar Lahadi ne yaron mai shekaru biyar ya fada cikin tsohuwar rijiyar da ta kafe, mai zurfin mita 40 a yankin Baoding dake Lardin Hebei.
Mahaifinsa ya shaidawa kafar yada labaran kasar Chinar cewa, yaron na taya shi tsinkar ganyyaye ne a gona, lokacin da lamarin ya faru.
Masu aikin ceton na ta amfani da motocin haka 60 da manyan motocin daukar kasa 100 wajen binciko yaron.
Har yanzu ba a san halin da yake ciki ba, amma ana aike masa da iskar shaka, da ruwa, da kuma abinci.
Rijiyar ta yi tsananin tsukewar da ke da matukar wahala wani babba ya shiga.
Bayan shafe kwanakin da aka yi ana haka, masu aikin ceton sun iya kai wa da mita 13 ne kawai zuwa kan wani karfe da a koda yaushe ka iya ruftawa,
Rijiyar ta shafe shekaru biyar ba a amfani da ita, kuma ba a saka wata alama dake nuna a yi hattara ba.