Boko Haram ta kashe wasu sojoji a arewa maso gabashin jihar Borno

'Yan Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojojin Najeriya na cigaba da fafatawa da kungiyar Boko Haram a yankunan jihar Borno

Rahotanni sunce an kashe wasu sojoji a daren ranar Litini bayan kungiyar Boko Haram ta kai hari a arewa maso gabashin jihar Borno.

Jami'an soji sun ce wasu sojojin sun jikkata a harin da aka kai kan sojojin da ke kauyen Kangarwa.

Harin dai yazo ne a daidai lokacin da sojojin Najeriya suka birne biyar daga cikin jami'anta ciki har da kanar Abu Ali wanda aka yaba saboda irin muhimmiyar rawar da ya taka a yaki da Boko Haram.

A karshen makon da ya gabata ne dai kungiyar mai ikrarin jihadi ta kashe Kanar Abu Ali da wasu jami'an sojin guda hudu a garin Malam Fatori.

A yammacin Litinin ne dai aka yi jan'izarsu.