'Yan Nigeria na goyon bayan Clinton a zaben shugaban Amurka

Hillary Clinton

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan Najeriya da dama na so Hillary Clinton ta zama shugabar kasar Amurka

'Yan Nigeria da dama na goyon bayan Hillary clinton, 'yar takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Democrat domin zamo wa shugabar kasa.

Mutane da dama a kasar sun damu cewa akwai yiwuwar hana shiga kasar, idan har Donald Trump abokin hamayyarta ya ci zaben.

Tuni dai Wole Soyinka, shahararren marubucin nan ya ce zai yaga takardarsa ta Green Card, wadda ke ba shi damar zama a Amurka kuma ya bar kasar idan har Mista Trump ya yi nasara.

Har ila yau dai 'yan Najeriyan na tsoron makomar 'yan uwansu da ke zaune a Amurka, da kuma irin tasirin da zai yi a kan rayuwarsu idan Donald Trump ya lashe zaben.

Najeriya dai na cigaba da fuskantar matsin tattalin arziki da tsada rayuwa.

Mutane da dama na dogaro ne da 'yan uwansu da ke kasashen waje domin su tallafa musu.