Biritaniya: Yarima Harry ya ce Meghan ce budurwarsa

Yarima Harry da budurwarsa Meghan Markle

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Yarima Harry ya fito ya bayyana a hukumance cewa Meghan Markle ce budurwarsa

Yarima Harry ya tabbatar wa duniya cewa Meghan Markle budurwar sa ce.

Yariman ya fitar da wannan sanarwar ne a hukumance daga fadar Kensington, inda ya soki kafofin yada labarai kan yadda suka yi ta tsangwamar budurwar tasa.

Sanarwar ta ce masoyan biyu, sun yi watanni hudu da fara soyayyar tasu, kuma bai kamata a sanya Misis Markle a gaba da zage-zage ba.

Yariman ya kara da cewa, shi bai cika daukan mataki a hukumanci kan rade-radin da basu da tushe ba, amma a cewarsa, wannan karon ture ya kai bango.

A 'yan kwanakin da suka wuce, jaridun kasar sun yi ta yada labarai kan Misis Markle mai shekaru 35, wacce aka fi sani da Rachel Zane, saboda fitOwar ta a wani shirin talabijan mai suna 'Suits'.

Dangantakar Yarima Harry da manema labarai ya dade da yin tsami dai, tunda ya dade yana yi masu kallon suna yi wa masarautarsu shisshigi dayawa, har dai yadda suka shiga rayuwar mahaifiyarsa, marigayiya Diana, Gimbiyar Wales.

A lokacin da ya ke da shekaru 20 kuma, an dauki hoton sa yana fada da masu daukan hoto a wani wajen shakatawa a London.

A shekarar 2012 kuma an fitar da wasu hotunan sa tumbur babu kaya, a wani otal da ke Las Vegas a Amurka.

Amma kuma Yarima Harry ya fice matuka wajen ayyukan sa na bayar da agaji, da kuma jaruntakarsa a ayyukan soja.