Niger: 'Yan bindiga sun kashe sojoji biyar a Nijar

Bayanan sauti

Wakilin BBC Baro Arzika ya aiko mana da wannan rahoton

Akalla sojoji biyar ne aka kashe, a yayin da wasu hudu kuma suka bace bayan wani hari da aka kai garin Banibangu da ke jihar Tilabery a Jamhuriyar Nijar.

Rahotannin da aka samu daga yankin Banibangu da ke jihar Tilabery wanda ke iyaka da kasar Mali, na cewa wasu 'yan bindiga ne suka kai wa garin hari.

Ya zuwa yanzu dai ba a tantance ko su wanene suka kai harin ba, amma ana zargin mayakan sun fito ne daga Malin.

Za ku iya sauraron karin bayani a rahoton da wakilinmu Baro Arzika ya aiko mana a farkon wannan shafi.