Zaben Amurka: Donald Trump ya kai kara kotu

Asalin hoton, Getty Images
Donald Trump ya yi zargin magudi a baya
Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya shigar da karar wani jami'in zabe a jihar Nevada, yana zargin cewa an bar rumfar zabe a bude fiye da lokacin da aka tsara.
Sai dai alkalin kotun, Gloria Sturman, ya yi watsi da karar, bisa la'akari da hadarin da ke tattare da bayyana sunayen masu aikin zabe.
Lauyoyin Mista Trump sun nemi ka da a hada takardun zaben da aka kada da wuri da na lokacin zabe na bai daya.
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a a jihar Nevada ta nuna cewa 'yan takarar biyu na tafiya kan-kan-kan.
Rahotanni daga sassan kasar da dama sun ce jama'a sun fito sosai domin kada kuri'unsu, inda aka kafa dogayen layuka.
Dukkansu sun yi kokarin jan hankalin masu kada kuri'a a jihohin da ake ganin takarar ta fi zafi da suka hada da North Carolina da Pennsylvania da Michigan.
Hillary Clinton ta nemi jama'a da su nuna karfin zuciya, yayin da shi kuma Trump ya ce Amurkawa na da damar kawar da tsarin da ya "daurewa cin hanci gindi".
Misis Clinton dai na gaban Mista Trump da maki hudu kacal, a kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan wanda ya fi farin jini.