Donald Trump ya kama hanyar lashe zaben Amurka

Trump da jama'arsa
Bayanan hoto,

Clinton dai na gaban Trump da maki hudu a kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan wanda ya fi farin jini

Dan takarar jam'aiyyar Republican Donald Trump ya shiga gaban Hillary Clinton a fafutukar lashe muhimman jihohi domin zamowa shugaban Amurka.

Gidan talabijin na ABC ya yi hasashen cewa tuni ya lashe Florida, Ohio da North Carolina, yayin da Clinton ta jam'iyyar Democrat ta lashe Virginia.

Ana kan-kan-kan a jihar Michigan, wacce rabon da Republican ta lashe tun shekarar 1988.

Kasuwannin hannayen jari sun fadi tun bayan da alamu suka fara nuna cewa Misis Clinton na fuskantar koma baya.

Har ila yau ana sa ran jam'iyyar Republican za ta rike rinjayen da ta ke da shi a majalisar wakilan kasar.

Ana bukatar dan takara ya samu wakilai 270 daga cikin 538 (wato electoral college) domin samun nasara.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta BBC ta nuna cewa Clinton na gaban Trump da maki hudu kacal.

Da sanyin safiya misalin karfe 06:00 ne aka fara kada kuri'a a Gabashin kasar, sai dai tuni wasu kauyuka a jihar New Hampshire sun riga sun kada kuri'unsu.

Masu kada kuri'a a Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jama'a sun fito sosai domin kada kuri'unsu

Duka Misis Clinton da Mista Trump sun kada kuri'unsu a mazabu daban-daban a birnin New York.

An samu dogayen layuka a wasu jihohin, abin da ke nuna yadda jama'a suka fito sosai.

Wasu wuraren kada kuri'ar sun samu matsalolin na'ura, abin da ya haifar da jinkiri.

Duka 'yan takarar sun yi gangamin yakin neman zabe a jihohin North Carolina da Pennsylvania da kuma Michigan, inda nan ne takarar ta fi zafi.

Sai dai tuni Amurkawa miliyan 46 suka jefa kuri'unsu a jihohin da suka bude rumfunan zabensu kwanakki gabanin wannan ranar ta zaben gama-gari.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan asalin Latin Amurka masu amfani da yaren Spaniya, wadanda ke goyon bayan Hillary Clinto, sun fito sosai.

Hillary Clinton da Donald Trump sun zagaye kasar domin neman kuri'un jama'a a 'yan kwanakin da suka gabata.