Yadda Trump ya bai wa duniya 'ruwa'

Batu na baya-baya da ya tayar da kura shi ne zargin da Trump ya yi wa Hillary kan goge dubban sakonni imail

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mutane da dama sun yi wa Donald Trump kallon mai katobara a lokacin mahawarsa da Hillary

Zaben da aka yi wa Donald Trump a matsayin shugaban Amurka ya bai wa wasu mutane mamaki ganin yadda aka yi hasashen cewa ba zai kai labari ba.

Kuri'ar jin ra'ayin mutane a Amurka ta nuna cewa 'yar takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton ta ba wa abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican, Donald Trump, tazara a ranar jajiberin fara zabe.

Wannan dai bai zo wa mutane da mamaki ba ganin cewa a duk lokacin da aka gudanar da irin wadannan kuri'un na jin ra'ayin mutane a watanni shidan da suka gabata, alkaluma sun sha juya wa Donald Trump baya ko da kuwa sun nuna shi ne ya yi wa Hillary Clinto zarra da farko.

Da alama dai al'ummar Amurka ba za su so ganin Donald Trump yana shugabantar su ba kuma a duk lokacin da sa'a ta karkata wurin Trump, masu fada aji a harkar zaben kasar suna iya bakin kokarinsu wajen dakile hakan.

To idan dai wannan ne abin da ke faruwa a Amurka a yanzu haka, to da alama Hillary Clinton ce za ta lashe zaben shugaban kasar.

Sai dai kuma wani abu dangane da kuri'ar jin ra'ayin mutanen shi ne, ba a ji ra'ayin masu zabe ba kan martanin da suke mayarwa game da wankewar da Hukumar FBI ta yi wa Clinton ba dangane da batun goge dubban sakonnin imail da aka ce ta yi.

To amma wani abu shi ne, cin zabe a Amurka ba abu ne da ake la'akari da yawan kuri'ar da 'yan kasa suka kadawa mutum ba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Zaben Hillary Clinton da Donald Trump ya yi zafi sosai

Hakan na dogara ne da yawan johohin da mutum ya lashe da za su ba wa dan takarar damar lashe manyan mazabu 270.

Saboda haka, sakamakon kuri'ar jin ra'ayin mutanen da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa har yanzu Donald Trump zai iya cin zabe.

To amma fa dole ne sai 'yan jam'iyyar Republican din sun tashi tsaye wajen lashe mazabu a jihohi kamar Pennsylvania da Michigan da kuma Virginia, a inda Clinton take jan ragama.

Shi dai Mista Trump yana da dimbin masu goyon baya a tsakanin farar fata masu fada aji, a inda ita kuma Clinton take da masu mara mata baya masu yawa a tsakanin bakake da matasa.

Har wa yau, Donald Trump ba zai sakankance da irin yadda Hispaniyawa suka yi fitar farar dango wajen kada kuri'a ba duk kuwa da cewa shi ne mutumin da ya zaburar da su domin su fita su kada kuri'ar.

Sai dai fa sakamakon wa suka zaba sai an je kidaya tukunna.