Obama zai gana da Trump a fadar White House

Shugaba Barrack Obama ya gayyaci Donald Trump

Asalin hoton, OTHER

Bayanan hoto,

Shugaba Barrack Obama ya gayyaci Donald Trump zuwa fadar White House don tattauna shirin mika mulki a watan Janairu

A ranar Alhamis ne shugaba Barrack Obama zai karbi bakuncin Donald Trump a fadar White House a wani mataki na shirin mika mulki ga sabuwar gwamnati a watan Janairu.

Zababben shugaban Amurkar Donald Trump, da kuma abokiyar takarar sa Hillary Clinton da shugaban kasar mai barin gado Barack Obama sun bukaci Amurkawa da su hada kai don ciyar da kasar gaba.

An dai tafka zazzafar muhawara tare da jefa kalamai masu zafi a lokacin yakin neman zaben kasar.

A bangare guda kuma ana ci gaba da gudanar da zanga zanga a wasu manya biranen Amurkar.

Asalin hoton, OTHER

Bayanan hoto,

Birnin New York na daya daga cikin manyan birane da ake zanga zanga

Birnin New York na daya daga cikin manyan birane da ake zanga zanga inda dubban jama'a suka yi dandazo a gaban ginin Trump Tower dake birnin don nuna rashin jin dadin su akan wasu manufofin Mr Trump da suka hada da matsayin sa game da baki da 'yancin yan luwadi da kuma batun zubar da ciki.

Asalin hoton, OTHER

Bayanan hoto,

Dubban jama'a sun yi dandazo a gaban ginin Trump Tower dake birnin New York

Tun da farko Mista Donald Trump, ya ce zai saka muradun Amurka gaba da komai, amma zai yi adalci ga kasashen da ke da sha'awar tafiya tare da Amurka. Ya bayyan hakan ne a lokacin da ya ke jawabinsa na murnar samun nasara, sabon zababben shugaba na Amurka,

Trump ya kara da cewa ''Kowane Ba'amurke, zai samu damar yin cikakken amfani da baiwar da Allah ya yi masa. Mutane maza da mata da aka mance da su, yanzu ba za a mance da su ba''

Dan takarar Shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump, ne dai ya lashe zaben kasar da aka yi ranar Talata.

Mista Trump ya lashe zaben ne bayan da ya samu nasarar cinye kujerun wakilai sama da 270 a jihohi 50, a inda ya kayar da abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton.

Trump, wanda ya gabatar da jawabin amincewa da yin nasara, ya ce Clinton ta kira wo shi a wayar tarho inda ta taya shi muranr lashe zaben.

A cewarsa, zai mayar da hankali wajen ganin ya sake gina Amurka, yana mai cewa muradin kasar su zai sanya farko a kan komai.

Yadda Donald Trump ya samu nasarar zama shugaban kasa

Manhajar intanet dinka ba ta daukar irin wadannan bayanan. Dole ne ka mallaki manhaja ta zamani wacce ke amfani da Javascript domin ganin wannan shafin.

Ya kara da cewa zai yi aiki tukuru wurin hada kan jama'ar kasar, sannan ya nemi hadin kan wadanda suka yi adawa da shi.

Ya kuma sha alwashin ganin ya saka Amurka a gaba a duk huldar da zai yi da kasashen waje.

Sai dai ya ce zai yi alaka mai kyau ta mutuntaka da sauran kasashe.

Nasararsa ta zo da matukar mamaki saboda dukkan kuri'un jin ra'ayin jama'a sun nuna Clinton na bayansa.

Taswirar adadin kuri'un da Hilary Clinton ta samu

Jam'iyyar Democrat

Manhajar intanet dinka ba ta daukar irin wadannan bayanan. Dole ne ka mallaki manhaja ta zamani wacce ke amfani da Javascript domin ganin wannan shafin.

A daya bangaren kuma, jam'iyyar ta Republican ta sake rike rinjayen da take da shi a majalisun dattawa da na wakilan kasar.

Taswirar adadin kuri'un da Donald Trump ya samu

Jam'iyyar Republican

Manhajar intanet dinka ba ta daukar irin wadannan bayanan. Dole ne ka mallaki manhaja ta zamani wacce ke amfani da Javascript domin ganin wannan shafin.