Kasashen duniya sun mayar da martani kan zaben Trump

Kasashen duniya sun soma mayar da martani kan zaben da Amurkawa suka yi wa Donald Trump a matsayin sabon shugaban su.

Farai Ministar Biritaniya, Theresa May ta taya Donald trump murnar nasarar da yayi a zaben shugaban kasar Amurka bayan zazzafar yakin neman zaben da ya yi da abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton.

Theresa May ta ce zata bai wa zababben shugaban kasar hadin kai domin su yi aiki tare.

Bayanan hoto,

Theresa ta ce zata bai wa Donald hadin kai domin su yi aiki tare

Farai Ministar Biritaniya, Theresa May ta taya Donald trump murnar nasarar da yayi a zaben shugaban kasar Amurka bayan zazzafar yakin neman zaben da ya yi da abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton.

Theresa May ta ce zata bai wa zababben shugaban kasar hadin kai domin su yi aiki tare.

Kasar Turkiya ta yi maraba da Trump, kodayake ya yi kira a gare shi da ya mika masa Fethullah Gulen, Malamin nan dan Turkiyya wanda ke zaune a Amurka saboda zargin da ake yi masa na kitsa juyin mulkin da aka yi yunkurin yi a kasar a watan Yuli wanda bai yi nasara ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Erdogan ya bukaci a taso keyar Fethullah Gulen

Shi ma shugaban Tanzania, John Magufuli ya taya shugaban Amurka mai jiran gado murnar nasarar da ya samu, yana mai ba shi tabbacin ci gaba da kawance tsakanin kasashen biyu.

Yadda Donald Trump ya samu nasarar zama shugaban kasa

Manhajar intanet dinka ba ta daukar irin wadannan bayanan. Dole ne ka mallaki manhaja ta zamani wacce ke amfani da Javascript domin ganin wannan shafin.

A nasa bangaren, shugaban kasar Philippine Rodrigo Duterte ya yi san-barka ga Donald Trump.

Wani ministan kasar ya ambato Duterte na cewa "Yana sa ran yin aiki tare da sabuwar gwamnatin domin inganta dangantaka tsakanin Philippines da Amurka ta hanyar mutunta juna da cin gajiyar juna da kuma tabbatar da dimokradiyya da mulki na gari a tsakanin mu."

Shi ma Firai Ministan New Zealand John Key ya taya Mr Trump murna, yayin da takwaransa na Australia Malcolm Turnbull ya ce Amurkawa "sun fahimci cewa ba su da aminai kamar 'yan Australia".