Trump: Shin Soyinka zai yaga katinsa na zama a Amurka?

Wole Soyinka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A matsayin shi na shahararren marubuci, ba lallai ba ne Wole Soyinka ya fuskanci matsala wajen samun katin green card

Tambayar da 'yan Najeriya ke yi bayan Donal Trump ya lashe zaben shugaban Amurka ita ce: Shin shahararren marubucin nan na Najeriya, Wole Soyinka, zai yaga katinsa na shaidar zama a Amurka (green card), kamar yadda ya sha alwashin, idan Trump ya ci zabe?

A kwanan baya ne dai Mista Soyinka ya ce ba lallai ba ne Trump ya ci zaben, a lokacin da yake jawabi a jami'ar Oxford da ke Birtaniya.

Ya kara da cewa amma kuma idan har ya ci, to abu na farko da zai fada shi ne "duk masu katin shaidar zama a Amurka na green card sai sun sake neman izini".

Jaridar Guardian ta ambato Soyinka yana cewa "Ni ba zan jira wannan ba."

Ya kara da cewa "Da zarar sun sanar da nasarar shi, zan yaga kati na da kai na, sannan na fara tattara kayana".

Mista Soyinka dai Malami ne a cibiyar nazari a kan harkokin Afirka da Amurka da ke jami'ar New York.

Shi ne mutumin Afirka na farko da ya samu lambar yabo na Nobel a kan rubutun adabi a shekarar 1986.