Hari ta sama ya kashe mutum 16 a Raqqa

Garuruwan Syria
Bayanan hoto,

Farar hula da dama suna barin yankunan da ke arewacin Raqqa

Harin saman gamayyar rundunar kawancen da Amurka ke jagoranta ya yi sanadin mutuwar akalla farar hula 16 a wani kauye a arewacin Raqqa na Syria inda 'yan kungiyar IS ke da karfin iko, a cewar masu fafutika.

Kungiyar kare hakkin bil adam ta Burtaniya da ke da cibiya a Syria ta rawaito cewa mata 6 da wani yaro na cikin wadanda suka rasa rayukansu a harin da aka kai a al-Heisha cikin dare.

Gamayyar mayakan Kurdawa da Larabawa wadanda Amurka ke mara wa baya, wadanda ke son kwace Raqqa na kai hari kan kauyen da ke karkashin ikon kungiyar IS.

Gamayyar rundunar kawancen ta ce tana duba rahotanni kan lamarin.

Mai magana da yawun kungiyar gamayyar kurdawa da larabawa ta yi watsi da batun.

Jihan Sheikh Ahmed ta gaya wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, "Babu wani abu makamancin haka da ya faru, kuma duk wanda ya yi irin wannan ikirari, to labarin IS kawai yake bayarwa."