Buhari da shugabannin Afirka sun taya Trump Murna

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai yi aiki tare da Trump domin karfafa dangantakar kasashen biyu

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Donald Trump, zababben shugaban Amurka murnar nasar zaben da yayi mai cike da mamaki.

Muhammadu Buhari ya ce a madadin gwamnatin Najeriya da mutanen kasar baki daya yana taya mista Trump murna.

Shugaban ya kara da cewa yana sa ran yin aiki tare da Donald Trump domin karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Shi ma a na sa bangaren, shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar ya taya Donald murna. Issoufou ya bayyana hakan ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter.

Haka zalika shugaban Ghana, John Mahama, ya wallafa sakon murna a shafinsa na twitter kamar yadda shi ma Macky sall ya taya zabben shugaban kasar Amurkar murna.

Shugaba Macky Sall ya ce a shirye Senegal take ta cigaba da karfafar dangantakar da ke tsakaninta da Amurka.

Shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo, Joseph Kabila, ya ce Trump ya samu gagarumar nasara kuma a shirye yake ya yi aiki da zababben shugaban domin karfafa dangantaka da kawance da ke tsakanin kasarsa da Amurka.