Kamfanin Shell ya rufe tashar Escravos a Nigeria

Yankin Nija Delta da ke kudancin Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mazauna yankin Nija Delta sun sha korafin barnar da kamfanonin man fetur ke yi ga muhallinsu

A Najeriya, kamfanin mai na Shell, ya ce ya rufe tashar samar da iskar gas ta Escravos da ke yankin Nija Delta mai azrikin man fetur.

Sanarwar na zuwa ne sakamakon zanga-zangar da wasu mazauna yankin suka yi a ranar Laraba.

A cikin wani sakon email da ya aikewa manema labarai, kamfanin na Shell din ya ce zai cigaba da ayyukansa a Escravos din idan masu zanga-zangar sun watse.

Masu zanga zangar sun kwashe kwanaki takwas suna gudanarwa, inda suka yi korafin rashin ababem more rayuwa a yankin.