Dubban mutane sun yi zanga-zangar kyamar Trump

An yi zanga-zangar kyamar Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Trump ya sha alwashin korar baki da Musulmi da 'yan Latino daga Amurka

Dubban masu zanga-zanga ne suka fantsama a kan titunan manyan biranen Amurka domin yin adawa da zaben Donald Trump.

Da dama daga cikin su sun rika yin ihu suna cewa "ba shi ne shugabanmu ba".

Wasu kuma sun rike mutum-mutumin Trump.

Mr Trump zai zama shugaban Amurka na 45 bayan ya lashe zaben da ya bai wa miliyoyin mutane mamaki inda ya doke Hillary Clinton.

Nan gaba ne zai gana da Shugaba Barack Obama a fadar White House domin tattaunawa kan yadda za a mika masa mulki.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An kona mutum-mutumin Trump

Mr Obama - wanda ya ce Mr Trump bai "cancanta" ya zama shugaban kasar ba sannan ya yi yakin neman kada a zabe shi - ya yi kira ga dukkan Amurkawa su karbi sakamakon zaben kamar yadda ya zo musu.

Ita ma Mrs Clinton ta shaida wa magoya bayanta su bai wa Trump damar jagorantarsu.