Ana zargin dakarun Iraq da kashe kauyawa

Myakan IS sun ce babu gudu babu ja da baya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An kaddamar da hare-hare domin kawar da IS daga Mosul

Kungiyar Amnesty International ta ce wasu maza da suka sanya kaya irin na 'yan sanda sun azabtar da mutane sannan suka kashe su a wasu kauyuka da ke kusa da Mosul.

Shaidun da kungiyar ta tattaro sun nuna cewa an harbe har lahira mutum shida a kauyukan Shura da Qayyarah bayan an kulle su a kan zargin suna da alaka da kungiyar IS.

Har yanzu hukumomi a kasar ba su komai a kan batun ba.

A watan jiya ne dakarun da ke goyon bayan gwamnatin kasar suka kaddamar da hare-hare na sake kwace Mosul daga hannun mayakan IS.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An tantance mutane da dama don ganin ko suna da alaka da IS

Jami'an tsaro kusan 50,000 - cikin su har da sojoji da 'yan sanda da mayakan Kurdawa na Peshmerga da Larabawa mabiya Sunna da 'yan Shia - na cikin wadanda ke fafatawa domin kawar da IS daga birnin.

Jami'an Amnesty sun ziyarci yankuna da dama domin ganin irin kisan gillar da ake zargin an yi wa mutane bayan mayakan IS sun janye daga yankunan, inda suka fitar da daruruwan mata da kananan yara da tsofaffi, wadanda a fili take cewa IS ta yi amfani da su ne a matsayin garkuwa.