Mourinho zai yi tankade da rairaya a United

Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mourinho ya lashe kofin Lig takwas a kasashe hudu

Kocin Manchester United Jose Mourinho yana yin bincike kan dukkan al'amuran da suka shafi kungiyar, yana mai cewa ya yi mamakin yadda ya gaji wasu abubuwa a kungiyar.

Rahotanni na cewa Mourinho bai ji dadin yadda ake tafiyar da sashen kula da lafiya na kungiyar ba.

An fahimci cewa bayan da ya karbi United daga hannun Louis van Gaal, Mourinho ya kula cewa tsare-tsaren kungiyar a fannoni da dama ba su kai yadda yake so ba.

Mourinho ya lashe kofuna 23 a lokacin da yake Porto da Chelsea da Inter Milan da kuma Real Madrid.

Ya fito fili ya tuhumi 'yan wasa Luke Shaw da Chris Smalling saboda rashin buga wasan da suka doke Swansea da ci 3-1 ranar Lahadi saboda raunin da suka ji, inda ya shaida wa manema labarai cewa: "Ya kamata mu inganta wannan kungiyar ta kowanne fanni."

BBC Sport ta fahimci cewa Mourinho, mai shekara 53, yana son yin garanbawul a kowanne bangare, ciki har da fannin zirga-zirga da zuwa wasannin sada zumunci da motsa jiki da kimiyyar wasanni da tsarin zuba 'yan wasa.

A farkon kakar wasa ta bana, tsohon kocin na Chelsea ya yi hasashen cewa United za ta yi gogayya wajen cin kofin Premier.

Sai dai galabar da suka yi a kan Swansea, wacce ke ta biyun karshe a tebirin Premier, ita ce nasara ta biyu da suka yi a wasanni takwas da suka yi a Premier.

Yanzu dai su ne a matsayi na shida a gasar - inda suke bayan ja Liverpool, wacce take ta daya, da maki takwas.