An kashe 'yan kunar-bakin-wake a Maiduguri

Hari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A makon jiya ma an kai hari a Maiduguri

Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno da ke Najeriya na cewa an kashe wasu 'yan kunar-bakin-wake da suka yi yunkuri tayar da bama-bamai da safiyar Juma'a.

Jamai'an tsaro sun shaida wa BBC cewa maharan uku, wadanda dukkan su mata ne, sun yi yunkurin shiga birnin Maiduguri ne amma an ci lagonsu aunguwar Ummurari da ke wajen birnin.

Kungiyar Boko Haram ce dai ke kai hare-hare a birnin da ma wasu yankuna na jihar ta Borno da makwabtan jihohi.

Sai dai rundunar sojin Najeriya ta ce tana ci gaba da fatattakar mayakan kungiyar, kuma nan ba da dadewa ba za ta kawar da ita daga doron kasa.

Ko a makon jiya sai da mayakan kungiyar suka kashe wasu sojin Najeriya, cikin su har da Latftanar Kanar Muhammad Abu Ali, wani soja da ya yi suna wajen ragargazar mayakan Boko Haram.