Ba ni da wata damuwa - Hamilton

Lewis Hamilton

Asalin hoton, Getty Images

Zakaran tseren motoci na duniya Lewis Hamilton ya ce ba zai damu ba idan ya yi rashin nasara a wasan da za a yi a Brazil, a kokarinsa na hana Nico Rosberg lashe gasar ta bana.

Abokin wasansa na tawagar Mercedes, Rosberg, wanda ke kan gaba da maki 19, zai lashe gasar ta bana idan ya samu nasara ranar Lahadi.

Hamilton bai taba lashe tseren motoci a Brazil ba, amma a nan ne ya lashe kofinsa na farko a 2008.

Dan tseren na Birtaniya ya ce, "Na fuskanci abubuwa da dama a nan. Samun nasara a nan na da matukar wahala, amma hakan shi ne burina".

Ana sa bangaren Rosberg cewa ya yi fatansa kawai shi ne al'amura su yi masa kyau a karshen mako.