Nigeria: An yi watsi da kasafin kudin hukumar tara haraji ta FIRS

'Yan majalisar dattawa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan Najeriya da dama na zargin cushe a kasafin kudin kasar na 2016.

Majalisar dattijai ta Nigeria ta yi watsi da kasafin kudin da hukumar tara kudin shiga ta kasar (FIRS) ta gabatar mata.

Majalisar tace ta yi hakanne saboda hukumar bata fayyace mata dalla-dalla abubbuwan da zata yi da kudaden da ta sa a kasafin kudin da ta gabbatar mata na wannan shekarar ba.

A ranar Alhamis ne dai 'yan majalisar suka yi watsi da kasafin kudin na hukumar tara kudi ta kasa

Hakan ya biyo bayan shugaban majalisar Bukola Saraki ya amince da shawarar da kwamitin kudin majalisar ya bayar.

Kwamitin ya ce hukumar tara kudi ta kasa bata zauna ta yi cikakken nazari ba kafin ta shirya kasafin kudin ta na wannan shekara.

Abinda yasa ta kasa bada cikakken bayanai kan irin manyan ayyukan da take son ta aiwatar, wanda kuma yasa hukumar tayi ta maimaita wasu ayyukan a kasafin kudin.

A wani jawabi da ya gabatar, Bukola Saraki yace a matsayin su na masu sa ido, "dole ne majalisar ta tabbata ta tattance duk ayyukkan da za'a aiwatar a kasar ta kuma tabbatar da cewa an kashe dai-dai kudin da ake bukata kan ko wanne aiki ba tare da anyi kari ba.

Bayan jawabin nasa ne dai 'yan majalisar sukayi watsi da kasafin kudin da murya daya.

'Yan Najeriya da dama na zargin cushe a kasafin kudin kasar na 2016.

Hakan ne dai yasa shugabannin majalisar dattijan kasar sukayi wa 'yan kasar alkawarin tabbatar ba a yi wani cushe ba a kasafin kudin kasa ko na wata ma'aikata.

Masana na ganin wannan matakin da 'yan majalisar suka dauka zai iya kawo tsaiko wajen aiwatar da aiyukkan hukumar ganin cewa ta gabatar da kasafin kudin a makare.