Ana ci gaba da boren kin jinin Trump a Amurka

An shiga dare na biyu da zanga-zangar kin amincewa da sabon shugaban Amurkar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An shiga dare na biyu da zanga-zangar kin amincewa da sabon shugaban Amurkar

An shiga dare na biyu na zanga-zanga a wasu biranen kasar Amurka, tun bayan sanar da Donald Trump a matsayin zababben shugaban kasar, sai dai wannan karon babu mutane kamar ranar farko.

Magajin birnin Los Angeles Eric Gercetti ya yi allawadai da tsirarun mutanen da suke toshe titunan birnin da suka haddasa cunkoson ababen hawa, sai dai ya jinjinawa wasu masu boren da abinda ya kira nuna yadda mulkin dimukradiya ya kamata ya kasance.

Tun da farko Mista Trump ya gana da shugaba Obama a fadar White House, don tattauna batun karbar mulki.

shugabannin sun tabo batutuwa da dama suka hada da batun cikin gida da kuma manufofin kasar kan kasashen waje.

Shugaba Obama wanda ya yi takaitaccen bayani ga manema labaru ya ce yana son Mr Trump da matarsa su ji cewa sun sami kyakkyawar maraba inda ya jaddadawa zababben shugaban kasar cewa za su yi duk abinda za su iya yi domin taimaka masa samun nasara.