Amurka: 'Yar gudun hijira ta zama wakiliya a majalisa

Ilham Omar
Bayanan hoto,

Ita ce 'yar gudun hijira da ta kafa tarihi a siyasar Amurka

Wata 'yar asalin Somalia kuma 'yar gudun hijira ta kafa tarihi a Amurka, inda ta zama 'yar majalisar wakilan kasar.

Ta shai da wa BBC cewa yaki da tsangwamar musulmai bakar fata da ake yi a Amurkar na daga cikin abubuwan da zata fi bai wa fifiko.

An dai zabi Ilhan Omar mai shekaru 34, don ta wakilci jihar Minnesota a majasalisar wakilai.

Kuma ta shaida wa Bola Munsoro ta sashen turanci abubuwan da take so ta cimma a matsayin ta na wakiliyar al'uma.

Ita dai Ilham ta na da shekaru 12 suka isa Amurka ita da iyayen ta a matsayin 'yan gudun hijira, kuma ta fara makaranta ne daga aji shida na firamare.

Ta dai sha fuskantar tsangwama a wajen 'yan uwanta dalibai, saboda rashin iya turancin ingilishi.

Amma idan ta yi wa mahaifin ta korafi, ya kan bata kwarin gwiwa da cewa ta dage da karatu, matukar iya harshen ingilishi to za ta samu sassaucin tsangwama daga abokanta.

Burin Ilham dai a yanzu bai wuce ganin ci gaban 'yan uwanta 'yan gudun hijira da suke zaune a Amurka shekara da shekaru.