An kai hari ofishin jakadancin Jamus a Afghanistan

'yan kungiyar Taliban sun sha kai hare-hare

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto,

A baya 'yan kungiyar Taliban sun sha kai hare-hare irin wannan a birnin

Wani bam da aka dasa a cikin mota ya tashi a ofishin jakadancin kasar Jamus da ke arewacin birnin Mazari sharif a Afghanistan, ya kuma hallaka mutane biyu.

Wani jami'in lafiya a asibitin yankin ya shaidawa BBC cewa an kawo fiye da fararen hula tamanin da suka jikkata asibiti, yawancin su kuma gilasan da suka farfashe ne suka ji musu raunin.

Mai magana da yawun kungiyar tsaro ta NATO a birnin ya ce an shiga da motar da aka makareta da bama-bama cikin ginin ofishin, lamarin da ya janyo mummunar barna.

Jim kadan da tashin bama-baman kuma sai aka fara harbe-harben kan mai tsautsayi, kuma tuni kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin.

Ko a baya ma 'yan kungiyar Taliban sun sha kai hare-hare irin wannan a birnin na Mazari Sharif, wanda shi ne birni na uku mafi girma a kasar.