India: Sabbin takardun kudi sun fara karanci

Takardun kudi na Rufi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bankunan sun fara korafin rashin isassun sabbin kudin

Jama'a sun sake yin jerin gwano a kofar bankunan kasar India, saboda kokarin sauya tsaffin takardun kudin kasar da sabbin bugawa.

Wakilin BBC a birnin Kolkata ya ce yawancin shaguna a birnin ba su yi ciniki ba saboda abokan huldarsu ba su da kudade a hannu.

Wakilin ya kara da cewa an bi tsari a dogon layin da ke bankuna a jiya alhamis, amma daga bisani sai mutane suka fusata saboda bankunan sun fara sanar da cewa sabbin takardun kudin na gab da karewa.

Firaiminista Narendra Modi dai bai wani sanar da batun sauyin kudin ba ga al'umar kasar, kwatsam sauyin ya faru a cikin makon nan a kokarin gwamnatinsa na ceto darajar kudin kasar Rufi daga sake durkushewa.

Harwayau a kasar ta India wata gobara ta tashi a kamfanin saka tufafi da ke wajen babban birnin kasar Delhi.

Mutane sha uku ne suka rasu a gobarar, kuma mai magana da yawun 'yan sandan birnin ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su ma'aikatan kamfanin ne da suke kwana a wurin.