Wenger ba ya son Chile ta sa Sanchez

Alexis Sanchez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alexis Sanchez ya ci wa Arsenal kwallo shida na gasar Premier a kakar wasa ta bana

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya bukaci Chile kada ta yi gangancin sanya Alexis Sanchez a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya da za ta yi da Uruguay.

Dan wasan mai shekara 27 bai buga wasan da Chile da Colombia suka tashi 0-0 ranar Alhamis ba saboda raunin da ya ji.

Jami'an kula da lafiya na Chile sun sa ran zai samu sauki kafin wasan da kasar za ta yi da Uruguay ranar Talata a Santiago.

Wenger ya shaida wa kafar watsa labarai ta beIn Sports cewa a kodayaushe Sanchez "Yana son buga wasa, kuma a shirye yake ya taka leda ko da kuwa lokacin da ya ji rauni ne."

Sanchez, wanda ya zura kwallo takwas a wasannin da ya buga wa Arsenal a kakar wasa ta bana, ya zaune a benchi kusan tsawon wata biyu a kakar wasan da ta wuce saboda raunin da ya yi.

Wenger ya kara da cewa "Batun rashin lafiyar tasa abu ne mai muhimmanci a tsakanin kungiyar kwallon kafar kasarsa da kuma kulob dinsa, amma dai ya kamata mu bai wa lafiyarsa muhimmanci."

Kocin na Arsenal ya ce za a dauki hoton wurin da dan wasan ya ji rauni domin sanin irin maganin da za a yi masa.