Dan wasan kokawar Gambia ya nutse a teku

Bahar rum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan Gambia na cikin wadanda ke yawan zuwa Turai

Kocin shahararren matashinan dan wasan kokawa na kasar Gambia ya ce dan wasan ya nutse lokacin da ya yi kokarin ketarawa zuwa turai daga tekun Bahar rum.

Ali Mbengu, mai shekara 22, ya gamu da ajalinsa ne lokacin da jirgin ruwan yake ciki ya kife yayin da suke hanyarsu ta zuwa Italiya daga Libya.

Wasan kokawa na da magoya baya sosai a Gambia da kuma makwabciyarta Senegal kuma hukumar kokawa ta kasar ta yaba wa marigayin a kan kwazon da ya nuna a wasan.

A farkon watan da muke ciki mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar ta rasu lokacin da ta yi kokarin ketara tekun bahar rum domin zuwa turai.