Kwayar cutar kwanputa ta 'kashe' shugaban Facebook

Mark

Asalin hoton, FACEBOOK

Bayanan hoto,

Shugaban Facebook na cikin wadanda aka ce sun mutu

Wata cutar da ake yadawa a kwamputa, wacce ta samu shafin Facebook, ta sa shafin ya sanar da mutuwar mutane da dama, ciki har da mai Mark Zuckerberg, mai kamfanin na Facebook.

Cutar dai ta sa shafin na sada zumunta ya wallafa wasu bayanai a shafukan Facebook na wasu mutane, wadanda za su nuna wa duk mutumin da ya ziyarci shafukan cewa mutanen fa sun mutu.

Hakan ya sa mutanen sun rika wallafa sakonnin da ke nuna cewa ba su mutu ba domin kawar da tashin hankalin da abokansu ka iya fada wa a ciki.

Kakakin kamfanin na Facebook ya bayar da hakuri a kan wannan gagarumin kuskure suka yi.

Ya kara da cewa,"Wannan ba karamin kuskure ba ne, amma dai mun gyara shi. Muna matukar bayar da hakuri a kan hakan."

A cewarsa, ana wallafa irin wadannan bayanai ne kawai a shafukan mutanen da suka mutu ta yadda abokansu da ke da rai za su rika tunawa da su, amma sai ga shi an ce mai kamfanin na Facebook na cikin wadanda suka rasu.

Sakon da aka wallafa a shafin Mr Zuckerberg ya ce "Muna fatan mutanen da ke kaunar Mark za su kwantar da hankalinsu sannan su rika tunawa da abubuwan na bajinta da ya yi a lokacin da yake raye."