Masu zanga-zanga na son shugabar Korea ta kudu ta sauka daga mulki

Masu zanga-zanga

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar sun bukaci a hukunta shugabar kasar

Dubban masu zanga-zanga sun taru a babban birnin Korea ta kudu, Seoul, inda suka bukaci shugabar kasar Park Gun-hye ta sauka daga kan mukaminta.

An girke 'yan sanda da dama a wajen zanga-zangar domin hana su zuwa fadar shugabar kasar.

Ana zargin Ms Park da kyale kawarta, Choi Soon-sil, ta yi mu'amala da muhimman takardun gwamnati ba tare da izini ba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Park ta amince cewa ta bar kawarta ta aikata laifi

Ana zargin cewa Ms Choi za ta yi amfani da takardun ne domin karbar makudan kudade daga wajen kamfanoni, kuma tuni aka tsare ta bisa zargin zamba-cikin-aminci da yin amfani da mukami ba bisa ka'ida ba.

Shugabar, wacce kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa farin-jininta ya yi matukar raguwa tun da aka fara wannan batu, ta ce "jikinta" ya yi sanyi.

A makon jiya ma sai da masu zanga-zangar suka taru a babban dandalin taro a tsakiyar birnin Seoul suna yin ihu da wake-wake, rike da wasu kwalaye da ke cewa "Dole Park Geun-hye ta yi murabus" da kuma "Dole a yanke mata hukuncin cin amanar kasa".