Jimoh Ibrahim ya yi watsi da hasashen TB Joshua

Jimoh Ibrahim

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto,

"Duk da cewa TB Joshua ya hango cewa ni ne zan zama gwamnan jihar Ondo, ina so ya yi hakuri ya rike hasashensa".

Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Ondo a Nigeria, Jimoh Ibrahim, ya yi watsi da hasashen da fitaccen malamin Kiristan nan TB Joshua ya yi cewa shi ne zai lashe zaben.

Mista Joshua ya samu sabani a hasashen da ya yi na cewa Hillary Clinton ce za ta zama shugabar Amurka amma kuma daga baya sai ya goge hasashen daga shafinsa na Facebook.

Jimoh Ibrahim, wanda ake kalubalantar takararsa a gaban kotu, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewar ba ya bukatar hasashen TB Joshua.

Ya ce "Duk da cewa TB Joshua ya hango cewa ni ne zan zama gwamnan jihar Ondo, ina so ya yi hakuri ya rike hasashensa".

Ya fitar da wannan sanarwar ce bayan Donald Trump ya lashe zaben Amurka, sakamakon hasashen malamin.

Wannan lamari dai na cigaba da jan hankulan mutane a Najeriya.

TB Joshua, wanda ke yawan jawo ce-ce-ku-ce, ya yi suna wurin iya addu'a da hasashe, kuma yana da dimbin magoya baya a ciki da wajen Najeriya.

A ranar 26 ga watan Nuwamba ne za a gudanar da zaben na jihar Ondo, inda takarar za ta fi zafi tsakanin jam'iyyun PDP mai mulkin jihar da kuma APC mai adawa.

Sai dai gwamnan jihar da mafiya yawan 'yan PDP ba sa goyon bayan Jimoh Ibrahim, kuma suna kalubalantarsa a gaban kotu.