Ambaliya ta kashe mutane a Afirka ta kudu

Mutane da dama sun rasa muhallansu a sanadiyyar ambaliyar
Amabaliyar ruwa ta mamaye birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu a wannan makon bayan an shafe watanni ana fama da fari
Mutane da dama sun rasa rayukansu yayin da wasu mutum 200 suka rasa muhallansu.
Wakilyar BBC, Nomsa Maseko ta ziyarci garin Alexandra, inda nan ambaliyar ta fi kamari inda wani mahaifi ya shaida mata cewa ambaliyar ta tafi da 'yarsa.
Masu aikin ceto dai suna cigaba da neman gawar yarinyar 'yar shekara uku.
Kungiyar bayar da agaji na taimakawa marasa galihu da abinci sai dai ya zuwa yanzu babu wata masaniya a kan inda za su kwana a daren ranar Asabar.