Mexico ta casa Amurka

Dan wasan Mexico Rafael (daga bangaren hagu) yana murnar kwallon da ya ci

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dan wasan Mexico Rafael (daga bangaren hagu) yana murnar kwallon da ya ci

Kasar Mexico ta doke Amurka da ci 2-1 a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya.

Kyaftin din Mexico Rafael Marquez ne ya zuwa kwallon da ta ba su nasara a minti na 89.

Wasan wanda aka yi a Columbus, jihar Ohio ya zo da wani batu domin kuwa an yi shi ne bayan Donald Trump, mutumin da ya sha alwashin gina katanga tsakanin Amurka da Mexico, ya lashe zabe.

Mexico ta ci kwallonta ta farko ne ta Miguel Layun, kodayake dan wasan Bobby Wood ya farke bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Nasarar da Mexico ta yi ta kawo karshen kashin da suka sha sau hudu a Ohio - jihar da take da muhimmanci, kuma wacce Trump ya ci zaben ta - domin kuwa tun shekarar 2001 suke kokarin cin wasa a jihar.