Nigeria: 'Ba a bai wa Kanar Abu Ali isasshen hutu ba'

Bayanan sauti

Ku saurari rahoton Nura Muhammad Ringim kan wannan batu:

'Yan uwan marigayi Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, kwamandan rundunar sojin kasar ta 272 mai kula da tankokin yaki, da 'yan Boko Haram suka kashe a jihar Bornon Najeriya sun zargi rundunar sojin kasar da rashin ba shi hutu.

Amina Abu Ali, kanwar Muhammad Abu Ali, ce ta yi wannan koke lokacin da wata kungiya mai rajin kare hakkokin sojin Najeriya da suka rasa rayukansu a lokutan yaki ta je yi musu ta'aziyya a Kaduna.

A cewarta, "Muna fatan sojin Najeriya za ta kammala yaki da 'yan Boko Haram domin gudun ci gaba da asarar zaratan sojin kasar".

Ta kara da cewa ya kamata a canza lokacin da sojoji ke shafewa a fagen daga domin "idan sun dade a can akwai gajiya. Sojoji na nan ko'ina, ba wai wasu sojoji ne kawai za su yi wannan yakin ba".

Ta ce "Dan uwana ya zauna a Maiduguri tsawon shekara biyu, amma hutun mako biyu kawai aka ba shi."

BBC ta tuntubi Kakakin rundunar sojin kasa kan wannan zargi, amma har yanzu ba mu samu amsa ba.

Asalin hoton, Nigerian army

Bayanan hoto,

Muhammad Abu Ali ya rika samun karin girma akai-akai saboda jarumtarsa

A ranar Litinin din da ta gabata ne aka yi jana'izar Muhammad Abu Ali tare da wasu sojoji hudu.

Sun mutu ne lokacin da suke kokarin dakile wani harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a barikin sojin kasar na 119 da ke garin Malam Fatori a jihar Borno.

Kafin rasuwarsa, Kanar Ali ya taka rawa sosai wurin kwato wasu garuruwa daga hannun Boko Haram, abin da ya sa aka yi masa karin girma.

Baya ga iyalan Kanar Ali, sojoji da dama da ke fafatawa a yankin Arewa maso Gabas, na kokawa kan rashin musanya su da karancin samun hutu.