Hikayata: Labari kan yadda ake lalata ƙananan yara

A ci gaba da karanto muku gajerun labarai ukun da suka yi nasarar lashe gasar BBC Hausa ta farko ta rubutun kagaggen labari ta mata zalla, a wannan karon za mu kawo muku labarin "Sai Yaushe?".

Wannan labari ne ya zo na biyu a gasar.

Baya ga ukun da suka fi fice kuma, sannu a hankali za mu kawo muku wasu labaran 12 wadanda alkalan gasar suka zaba a matsayin wadanda suka cancanci yabo.

Ga dai marubuciyar Sai Yaushe? Amina Hassan Abdulsalam: