An bayyana 'yan takarar gwarzon kwallon Afirka na BBC

Pierre-Emerick Aubameyang, da Andre Ayew, da Riyad Mahrez, da Sadio Mane da kuma Yaya Toure
Bayanan hoto,

'Yan takarar Zakaran Kwallon Afirka na BBC na 2016

An bayyana 'yan takarar su biyar a wani taro na musamman da aka yi domin kaddamar da gasar Zakaran Kwallon Afirka na BBC ta bana a ranar Asabar.

Masoya kwallo daga sassa daban-daban na duniya ne za su zabi wanda zai lashe kyautar ta hanyar latsa wannan shafin.

Kuma suna da dama, daga yanzu har zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba da karfe 6:00 na yamma agogon GMT, su zabi gwaninsu.

Ranar Litinin, 12 ga watan Disamba ne za a bayyana sunan wanda ya lashe kyautar kai-tsaye a BBC Focus on Africa talabijin da rediyo. Mu ma a Sashen Hausa za mu ba da sanarwar kai-tsaye a shafin mu na BBC Hausa Facebook.

Shafin mu kuma na bbchausa.com ma zai dauki sanarwar gwarzon da ya lashe kyautar. Za ku iya duba ka'idojin zaben anan.

Aubameyang dai na cikin takarar a karo na hudu ke nan a jere, shi ma gwanin da ya lashe a 2011 Ayew, yana fitowa a karo na hudu ke nan.

Mahrez ne kadai dan wasan da ba a taba zaba ba a baya, shi kuma Mane wannan ne karonsa na biyu a takarar, kazalika gwarzon da aka zaba har sau biyu Toure, ya jera shekaru takwas yana takara a gasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pierre emerick-Aubameyang yana matukar haskakawa a gasar lig ta Jamus

Dan wasan gaba gaban kuma dan kasar Gabon Aubameyangna da fitattun kwallaye 26 da ya sha wa kulob dinsa Borussia Dortmund a 2016.

Aubameyang ya zamo dan Afirka na farko da aka bayyana a matsayin Gwarzon dan wasan shekarar, kuma dan Gabon na farko da ya lashe Gwarzon Dan Kwallon shekara na Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka, kuma yana cikin zababbun 'yan takarar kyautar gwarzon kwallo ta Ballon d'Or.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Andre Ayew na fatansake lashe wannan gasa a karo na biyu

A watan Agusta West Ham ta kashe makudan kudaden da ba ta taba kashe irinsu ba a baya wajen sayen dan Ghana Andre Ayew daga Swansea, a kan kudi fam miliyan ashirin da dubu dari biyar.

Ficen da Ayew ya yi a fagen buga kwallo, da kuma jimillar kwallaye 12 da ya ci a wasanni 35 a tsakanin shekarar 2015 da 2016, sun sanya shi yin fice a karshen kakar wasanni, inda ya samu kyautar gwarzon sabbin 'yan wasa a watan Mayu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Riyad Mahrez da kasarsa Algeria suna taka rawar gani

Dan wasan Leicester City, kuma dan kasar Algeria Mahrez, ya samu nasara matuka a kungiyarsa wadda ba wanda ya taba zaton za su kai inda suka kai, inda suka dauki Kofin Gasar Premier a karo na farko.

Mahrez ya ci kwallo 17 a wasannin tsakanin 2015 da 2016, kuma shi ya lashe kyautar Gwarzon Kwallon Kafar Shekara na kwararru.

Shi ne kuma dan Afirka na farko da ya lashe kyautar. Ya kuma buga wa Algeria kwallon cancantar shiga kwallon kafar duniya ta 2017.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sadio Mane na taka rawar gani sosai a Senegal da Liverpool

Dan wasan na gaba dan kasar Senegal ya zamo dan kwallon Afirkan da ya fi kowanne tsada a tarihi lokacin da ya koma Liverpool a kudi fam miliyan 34 a bana.

Ya yi fice sosai a Anfield, bayan da ya zira kwallo 11 a wasannin da suka buga da Manchester United, inda daga bisani ya ci gaba daga inda ya tsaya a Southampton - inda ya sha kwallo takwas a 2016 da Saints, ciki har da kwallo uku da ya ci a wasa guda (wato hat-trick) a lokacin da suka kara da Manchester City.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yaya Toure ya taimaka wa Ivory Coast ta lashe gasar cin kofin Afirka a 2015

Toure dai shi ya sake lashe kofi a 2016 - a karo na 17 a rayuwarsa ta kwallo - lokacin da ya daga Kofin Gasar League ta Ingila da Manchester City, bayan ya sha kwallo a fanariti da suka yi nasarar kan Liverpool a wasan karshe.

A wannan shekarar ne dan wasan tsakiyar mai shekaru 33 ya ce ya kawo kololuwar rayuwarsa a kwallo, duk da ya ce har yanzu da sauransa, kuma sanya shi da aka yi cikin wadanda za su buga wasannin shekara mai zuwa ya tabbatar da hakan.