Ka'idoji da sharudda na zaben Gwarzon Kwallon Afirka na BBC

Pierre-Emerick Aubameyang, da Andre Ayew, da Riyad Mahrez, da Sadio Mane da kuma Yaya Toure
Bayanan hoto,

'Yan takarar Zakaran Kwallon Afirka na BBC na 2016

A ranar Asabar ne aka sanar da sunayen 'yan wasan da aka ware don zabo Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC na 2016 yayin wani shiri na musamman wanda za a yada kai-tsaye a rediyon BBC World Service, da tashar talabijin ta BBC World News, da kuma shafukan intanet da na sada zumunta na BBC.

Ga karin bayani da sharuddan kada kuri'a a kasa.

Matakin zabo wadanda aka ware sunayensu

Fitattun kwararru a kan harkar Kwallon kafa a fadin nahiyar Afirka ne suka zabo mutane biyar din da aka ware sunayensu. An bukaci masanin harkar kwallo daya a ko wacce kasa ya fadi 'yan wasa ukun da suka fi cancanta ba tare da la'akari da matsayin da ya ajiye ko wanne ba.

An bukace su ne su zabo 'yan bisa la'akari da wadannan sharudda: hazikanci; iya rike kwallo; iya aiki-tare; dogewa; samar da kyakkyawan sakamako da kuma iya wasa ba da gaba ba a kakar wasanni ta 2015/2016.

Za a sanar da jerin sunayen wadanda aka ware yayin wani shiri na musamman da za a yada kai-tsaye a gidan rediyon BBC World Service da tashar talabijin ta BBC World ranar Asabar 12 ga watan Nuwamba daga karfe 6:05 na yamma agogon GMT zuwa karfe 7:00 na yamma agogon GMT. The shortlist will be announced during a special live launch programme on Saturday 12 November from 1805-1900 GMT on BBC World Service and BBC World TV. Za kuma a yada a intanet a www.bbc.com/africanfootball.

Idan aka samu mutum fiye da daya sun yi kankankan a matakin ware mutum biyar, tawagar masu shirya bayar da kyautar Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na da hurumin kara yawan 'yan takara zuwa mutum shida matuka.

Ta'arifin wanda ya cancaci takara

Mutanen da suka cancanci takarar Gwarzon Kwallon Kafar Afirka su ne wadanda suka cancanci taka leda a wata tawagar kwallon kafa ta kasashen Afirka.

Kada kuri'a

Da zarar an sanar da sunayen wadanda aka ware su yi takara, jama'a za su zabi wanda za a bai wa kyautar ta hanyar kada kuri'a a intanet.

Za a kaddamar da wannan mataki na kada kuri'a da misalin karfe 6:50 na yamma agogon GMT ranar Asabar 12 ga watan Nuwamba 2016 a kuma rufe da karfe 6:00 na yamma agogon GMT ranar Litinin 28 ga watan Nuwamba 2016.

Za a sanar da sakamakon zaben kai-tsaye da karfe 5:35 na yamma agogon GMT ranar Litinin 12 ga watan Disamba a tashoshin rediyo da talabijin na BBC Focus on Africa. Za kuma a kafe sakamakon a shafin intanet na Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC tare da dukkan sharudda da ka'idoji.

Idan wadansu suka yi kankankan to za a raba musu kyautar.

Yadda za a kada kuri'a - a internet

Za a kada kuri'a ne ta hanyar ziyartar shafin Gwarzon Kwallon Kafar BBC a www.bbc.com/africanfootball da kuma bin ka'idojin da aka zayyana. Kuri'a daya kacal za a iya kadawa a kan ko wacce na'urar kwamfiyuta.

Sharudda da ka'idojin kada kuri'a

1. BBC ke kula da wannan zabe kuma kyautar ta cika dukkan sharuddan da BBC ta gindaya na gudanar da gasa ko zabe wadanda za a iya karantawa a www.bbc.co.uk/editorialguidelines/guidelines/appendix2

2. Za a bai wa wanda ya yi nasara wani kambu mai dauke da rubutu sannan za ba shi lakabin Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC na Shekarar 2016.

3. Wadansu kwararru a kan harkar kwallon kafa a fadin Afirka ne suka zabo wadanda suke takarar zama Gwarzon Kwallon Kafar Afirka na BBC.

4. Sharuddan da aka yi la'akari da su wajen zabo 'yan takarar su ne: hazikanci; iya rike kwallo; iya aiki-tare; dogewa; samar da kyakkyawan sakamako da kuma iya wasa ba da gaba ba a kakar wasanni ta 2015/2016.

5. Za a ba jama'a damar kada kuri'a a shafin intanet na Gwarzon Kwallon Kafar Afirka a www.bbcworldservice.com/africanfootballer da www.bbc.com/africanfootball don zaben gwarzo a cikin 'yan takarar. Karkari a ko wacce na'urar kwamfiyuta za a kada kuri'a daya.

6. BBC za ta yi amfani da bayanan da kuka bayar don wannan zabe ne kawai kuma ba za ta wallafa su ko ta bayar da su ga kowa ba sai da izininku. Idan kuna neman karin bayani game da manufofin tsare sirri na BBC a www.bbc.co.uk/usingthebbc/privacy.

7. Lokacin rufe kada kuri'a shi ne karfe 6:00 na yamma agogon GMT ranar Litinin 28 ga watan Nuwamba 2016.

8. Abin da sakamakon ya nuna da shi za a yi aiki, babu wani korafi da za a saurara.

9. Wajibi ne duk wanda ya yi nasara ya karbi kyautar kamar yadda aka ayyana ba damar jinkirtawa. Ba kuma za a bayar da kudi a maimakon kyautar ba. Sannan ba za bai wa kowa kyauta don ya kada kuri'a ba.

10. BBC, da masu yi mata kwangila, da bangarorinta da/ko wakilta ba za su dauki alhakin duk wata matsala ta na'ura ko rashin samun intanet ko wani abu mai kama da haka da ka iya haddasa asarar kuri'a ba.

12. BBC na da hurumin soke kuri'a ko ma dakatar da zabe idan akwai dalilan da ke nuna cewa an yi magudi wajen kada kuri'a ko kuma an yi yunkurin tafka magudi. BBC na da hurumin sauya tsarin gudanar da zabe a duk lokacin da ta ga dama. BBC ba za ta wallafa wadannan bayanai ba ko ta mika su ga wani ba tare da izini ba sai idan haka ya zama dole don tabbatar da aiwatar da wadannan sharuddan. Don samun karin bayani a duba Manufar Tsare Sirri ta BBC a http://www.bbc.co.uk/usingthebbc/privacy/

13. Ana daukar duk wadanda suka kada kuri'a a wannan zabe da cewa sun amince da wadannan ka'idojin sun kuma yarda su yi aiki a kansu. A lura cewa ma'aikatan BBC ko ma wani wanda ke da alaka kai-tsaye da shirya wannan zabe bai cancanci kada kuri'a ba.

14. Sashen Afirka na BBC ne zai sa ido a kan harkar zaben.

16. BBC ta bar wa kanta ikon soke cancantar ko wanne dan takara ko ta ki ba shi kyautar idan a fahimtar ta yin hakan zai bata sunan BBC.

17. Dokokin Ingila da Wales na da karfi a kan wadannan ka'idojin.