Ina daraja sana'a ta— Hadiza Gabon

Ina daraja sana'a ta— Hadiza Gabon

A lokaci zuwa lokaci, masu ruwa da tsaki a harkar fina-finan Afirka, na karrama jarumai da suka fi yin bajinta, da nufin bunkasa sana'ar fina-finan. A bana, Hadiza Gabon, jarumar fina-finan Hausa a Najeriya, na cikin wadanda aka karrama da lambar yabo ta African Hollywood Awards a London. A hira da Haruna Shehu Marabar Jos, Hadiza Gabon din ta fafi dalilin da ya sa ta cancanci karrama wa.