Dan uwan Sarki Salman na Saudiyya ya rasu

King Salman of Saudiyya
Bayanan hoto,

Sarki Salman na Saudiyya

Rahotanni daga Saudiyya sun ce daya daga cikin 'yan uwan Sarki Salman na kasar, Yarima Turki bin Abdul Aziz ya rasu ya na da shekaru sama da tamanin.

Yariman, wanda tsohon mataimakin ministan tsaro ne, yana daga cikin 'yan uwa bakwai masu karfin fada aji, wadanda suka rike manyan mukamai a gwamnatin kasar na tsawon shekaru.

A shekarun 1970, Yarima Turki bin Abdul Aziz ya koma Masar da zama bayan wata takaddama a cikin iyalan gidansu sakamakon karin aure da ya yi.

Ya koma Saudiyyan ne bayan rasuwar matar shi.