Tsohon dan kwallon Ivory Coast Laurent Pokou ya rasu

Tsohon dan wasan kwallon kafa na Ivory Coast Laurent Pokou

Asalin hoton, MVISTATIC

Bayanan hoto,

Laurent Pokou ya kafa tarihi a gasar cin kofin Afirka

Tsohon dan wasan kwallon kafa na Ivory Coast Laurent Pokou, wanda ake wa kallon wani kusa a fagen kwallon kafa a nahiyar Afirka, ya rasu, yana da shekara 69.

Laurent Pokou ya taka leda daga shekarun 1960 zuwa 1970 a kungiyar ASEC Mimosas inda ya fara kwallonsa.

Ya buga wa kasarsa kwallo sau 70.

Pokou ya kuma buga kwallo a kulob din Nancy na Faransa daga 1977 zuwa 1978, inda ya yi wasa tare da Michel Platini.

Ana tuna shi saboda tarihin da ya kafa na zura kwallaye mafiya yawa - 14 - da wani dan kwallo tilo ya yi a gasar cin kofin kasashen Afirka.

Sai bayan shekara 30 sannan dan wasan Kamaru Samuel Eto'o ya shafe wannan tarihi a shekara ta 2008 a gasar da aka yi a Ghana.

Pokou ya mutu ne a birnin Abidjan bayan ya sha fama da rashin lafiya.