NATO ta gargadi Donald Trump

Dakarun tsaron NATO
Bayanan hoto,

Dakarun tsaron NATO

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO, ya gargadi zababben shugaban Amurka Donald Trump cewa matakin da ya ke shirin dauka kan dangantakar da ke tsakanin Amurka da tarayyar turai bai dace ba.

Mista Jens Stoltenberg ya yi wannan kalami ne a jaridar Observer ta Birtaniya, inda ya kara da cewa kasashen yammacin duniya na fuskantar kalubalen tsaro da aka dade ba a ga irin shi ba.

A lokacin yakin neman zabe, Mista Trump ya ce idan ya yi nasarar zama shugaban kasa zai sake nazari kan yiwuwar taimakawa kasashe kawayen Amurka da aka kai wa hari idan har ba ta biya abubuwan da suka zama hakki kasar ta biya ba a cikin kawancen NATO.

An kuma ambato mai magana da yawun shugaba Vladimir Putin na Rasha na cewa da Mista Trump zai matsawa NATO lambar janye dakarun su daga iyakar kasar Rasha, kuma tabbas za su kulla alaka mai aminci tsakanin su da Amurka.