Harin bom ya halaka fiye da mutane 50 a Karachi

Pakistan

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Rahotanni sun ce mutane 70 ne suka jikkata a harin

Jami'ai a Pakistan sun ce fiye da mutane 50 ne suka mutu sakamakon tashin bom a wani wurin ibada na Musulmai sufaye, a arewacin birnin Karachi.

Kafofin yada labarai na cikin kasar sun ce mutane da dama ne suka jikkata a harin.

Harin ya auku ne yayin da rana ke fitowa, lokacin da akalla mutane dari biyar suka taru a wurin ibadar domin gudanar da al'amuransu.

Motocin daukan marasa lafiya sun shafe sa'o'i kafin su isa wurin, amma daga baya, sun kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

An kai harin ne watanni bayan an harbe Amjad Sabri, wani fitaccen mawakin Sufanci a Karachi.