Faransa: An cika shekara guda da kai hare-hare

Shekara guda kenan tun bayan wasu masu ikirarin kishin Islama suka hallaka mutane 130 a birnin Paris

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Shekara guda kenan tun bayan wasu masu ikirarin kishin Islama suka hallaka mutane 130 a birnin Paris

Ana gab da fara bukukuwar cika shekara guda da kai harin da ya hallaka sama da mutane dari a birnin Paris.

Shugaba Francois Hollande da magajin birnin Paris ne za su jagorance daga tutar tunawa da wadanda suka hallaka a wurare shida da akai kai hare-hare mafi muni da kasar ta fuskanta cikin shekaru masu yawa.

Tun da farko Firaiministan Faransa Manuel Valls ya shaidawa BBC cewa mai yiwuwa a kara tsawaita wa'adin dokar ta bacin da aka sanya a kasar .

A halin yanzu an sake bude babban dakin kallon Sinima na Bataclan inda masu kallo suka yi shiru na minti daya don tunawa da mutane 89 da 'yan bindiga suka kashe a cikin wurin.

'Yan uwa da iyalan mutanen da suka mutu ne suka halarci gidan siniman.