Gagarumar girgizar kasa ta abka wa New Zealand

New Zealand na yankin da ke fama da girgizar kasa

Asalin hoton, USGS

Bayanan hoto,

New Zealand na yankin da ke fama da girgizar kasa

Hukumar da ke sanya ido kan sauyin yanayi ta Amurka ta ce wata girgizar kasa mai karfin 7.4 ta abka wa yankin Christchurch da ke New Zealand.

Ma'aikatar tsaro ta gargadi mutanen da ke gabar teku daga gabashin South Island su matsa daga yankin saboda yiwuwar faruwar tsunami.

Har yanzu dai birnin na Christchurch bai gama murmurewa daga girgizar kasar da ta abka masa a shekarar 2011 ba, wacce ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 185 sannan ta lalata tsakiyar birnin.

New Zealand dai tana yanki ne wanda ke da saurin faduwar girgizar kasa da tsagewar kasa.

Rahotannin farko sun nuna cewa wasu gidaje a garin Cheviot, kusa da tsakiyar wurin da girgizar kasar ta faru, sun lalace.

Wani mazaunin Christchurch ya ce girgizar kasar ce ta tashe su daga bacci, sakamakon rawar da gidaje suka rika yi.