Rikicin DRC: Jami'an MDD na ziyara a Beni

UN security Council

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mambobin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya

Wakilan kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na wata ziyara a yankin Beni da ke fama da tashe-tashen hankali a gabashin Jamhoriyar Dimukradiyar Congo, da nufin rage zaman dar-dar a kasar.

Daruruwan fararen hula ne aka kashe a yankin na Beni a cikin shekaru biyun da suka gabata.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce an yi biris da mutanen dake yankin.

A ranar Asabar, kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniyan ya shaidawa shugaba Joseph Kabila cewa, ya kamata ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar, ta hanyar sauka daga mulki idan wa'adinshi na karshe ya kare a watan gobe.

An dage zabukan kasar, sannan an yi ta samun tashe-tashen hankali a babban birnin kasar Kinshasa da sauran wurare.