Gwamnati ta yi lugudan wuta kan Musulman Rohingya

Myanmar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jami'in tsaro a Myanmar

Gwamnatin Myanmar ta amsa cewa, tayi amfani da jiragen helikofta na yaki wajen bude wuta a wasu kauyuka na Musulman Rohingya da basu da rinjaye a yammacin kasar.

Kafofin watsa labarai na kasar sun ce an bukaci daukin jiragen yakin ne bayan taho mu gama tsakanin sojoji da wasu da ake zargi 'yan bindiga na kabilar Rohingya ne, ta yi sanadin mutuwar mutane takwas, biyu daga ciki sojoji.

Jihar Rakhine, wacce ta hada iyaka da Bangledash, wuri ne da 'yan kabilar Rohingya da dama ke zaune, wadanda ake nuna wa wariya.

Wasu majiyoyi na kabilar Rohingya sun zargi sojojin kasar da yunkurin kawar da kabilarsu baki daya, sai dai gwamnatin kasar wacce Aung San Suu Kyi ke jagoranta, ta ce samamen da aka kai, wani bangare ne na neman wadanda suka kai harin.