Ana taro a kan sauyin yanayi a Morocco

Shugaba Buhari zai yi jawabi a wajen taron kan sauyin yanayi
Bayanan hoto,

Shugaba Buhari zai yi jawabi a wajen taron kan sauyin yanayi

A ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya domin halartar taron Majalisar dinkin duniya kan sauyin yanayi a birnin Marrakech na Morocco.

A yayin taron, Shugaban zai gabatar da jawabi kan matsayin kasarsa game da muhimman batutuwa da suka jibanci sauyin yanayin a ranar Talata yayin zaman farko na kaddamar da taron.

Kazalika shugaban na Najeriya zai kuma gabatar da bukatar kasarsa ta samun goyon bayan kasashen duniya wajen aikin share yankin Ogoni na Niger Delta da kuma kokarin farfado da tafkin Chadi.

Anasa ran taron zai hado kan shugabannin kasashen duniya da ministocin muhalli da wakilan kungiyoyin sa kai da na 'yan kasuwa daga kasashe 197, kuma shi ne na farko tun bayan muhimmiyar yarjejeniyar Paris wadda aka aiwatar a ranar 4 ga watan Nuwambar da muke ciki.