Trump da Clinton duk abu daya ne - Shekau

Abubakar Shekau

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jami'an tsaron Najeriya sun sha ikrarin kashe shi amma sai ya sake bayyana.

Shugaban daya daga cikin bangarorin kungiyar Boko Haram biyu da ake da su a Najeriya ya ce ko da Hillary Clinton Amurkawa suka zaba a zaben shugaban kasa na makon jiya sun yi hasara.

A cikin wani sakon murya da wani makusancinsa ya aiko wa sashen Hausa na BBC, Abubakar Shekau ya ce a shirye suke su kalubalanci manufofin zababben shugaban na Amurka.

Ya kuma yi Allah-wadai da matakin da ya ce sarkin Saudiyya mai bin tsarin shari'ar musulunci ya dauka na yin maraba da zaben Mr Trump.

Ya yi amfani da wannan damar wajen daukar alhakin kai munanan hare-hare kan dakarun Najeriya a wasu sassan jihar ta Borno a kwanannan wanda ya hallaka da dama daga cikinsu.

Shekau ya dade yana sukar manufofin hukumomin Amurka da Saudiyya da kuma Najeriya.

Kimanin mutane 30,000 ne suka mutu sakamakon rikicin Boko Haram. Sannan wasu fiye da miliyan biyu suka rasa muhallansu.