Tsohon Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki ya rasu

Alhaji Ibrahim Dasuki
Bayanan hoto,

Marigayi Dasuki ya dauki lokaci mai tsawo yana jinya.

Allah ya yi wa Mai alfarma Sarkin Musulmi na 18 a daular Usmaniyya da ke Najeriya Alhaji Ibrahim Dasuki rasuwa.

Marigayi Ibrahim Dasuki ya rasu ne ranar Litinin da daddare a wani asibiti da ke birnin Abuja yana mai shekara 93.

Wata majiya a fadar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato ta shaida wa BBC cewa tuni aka fara shirye-shiryen jana'izarsa kuma ana sa ran gudanar da ita da misalin karfe 2:00 na ranar Talata a birnin na Sakkwato.

Alhaji Ibrahim Dasuki, wanda shi ne mahaifin tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan al'amuran tsaro, Kanar Sambo Dasuki, ya rasu ya bar 'ya'ya da jikoki masu yawa.

Sarautar Sarkin Musulmi

Marigayi Ibrahim Dasuki ya zama Sarkin Musulmi ne a watan Disambar shekara ta 1988 bayan rasuwar Sarkin Musulmi na 17 Alhaji Abubakar Sadik na 3.

Ya kwashe shekaru takwas kan mulki kafin gwamnatin soji ta Marigayi Janar Sani Abacha ta sauke shi a shekara ta 1996.

An zarge shi da kin bin umarnin gwamnati da kuma yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ba tare da neman izni ba.

Bayan sako shi daga inda aka tsare shi tsawon shekaru, ya tare a gidansa da ke birnin Kaduna inda ya ci gaba da tafiyar da harkokin rayuwarsa har zuwa lokacin ya kamu da cutar ajali.

Sumamen jami'an tsaro

Sanar da shi a zaman magajin Sarki Abubakar na III a maimakon dansa Alhaji Muhammadu Maccido Abubakar III ya jawo wata zanga-zanga ta tsawon kwanaki biyar a birnin na Sakkwato wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla goma.

Masu adawa da nadinsa a lokacin na ganin Muhammad Maccido mai ra'ayin mazan jiya a zaman wanda ya fi cancantar da wannan kujerar bisa shi Alhaji Ibrahim Dasuki mai ra'ayin tafiya da zamani.

Marigayin ya nuna rashin jin dadinsa karara, lokacin da jami'an tsaro suka kai sumame gidansa na Sokkwato a lokacin da suke binciken dansa Sambo Dasuki.

Shi dai Sambo, wanda tsohon mai baiwa Shugaba Goodluck Jonathan shawara ne kan harkokin tsaro, yana fuskantar shari'a kan zargin cin hanci da rashawa.

Batun da ya musanta yana mai cewa siyasa ce kawai.