Obama na kokarin kau da fargabar kasashe game da Trump

Asalin hoton, Getty Images
Haka ma ya bukaci sabon shugaban da ya ja al'umomi marasa rijaye a jika.
Shugaban Amurka mai-barin-gado Barack Obama na kokarin tabbatar wa kasashe kawayen Amurka cewa Donald Trump zai mutunta kawance daban-daban da kasar ke ciki idan ya karbi mulki a watan Janairu.
A yayin wani taron manema labarai gabanin tafiyarsa ta karshe zuwa wata kasar waje a zaman shugaban kasa, Mr. Obama ya ce Mr. Trump ya nuna sha'awar ci gaba da kasancewar Amurka a kungiyar NATO.
A lokacin yakin neman zabe dai Donald Trump ya jefa shakku a zukatan kawayen Amurka na ko zai bar kasar ta ci gaba da zama a kungiyar ta NATO idan ya ci zabe, yana mai nuna bacin ransa ga yadda kasashen da dama da ke cikin kawancen ba su kashe kashi 2% na kudaden shigarsu kan tsaro- wanda sharadi ne ga zamowar kasa wakiliya a kawancen.
Amma shugaba Obama wanda ke kan hanyarsa ta ziyartar kasashen Jamus da Girka da kuma Peru ya ce daya daga cikin muhimman ayukkan da zai yi yayin wannan ziyarar shi ne bayar da tabbacin cewa Mr. Trump na goyon bayan zaman kasar a kungiyar ta NATO.