Yara na fuskantar karancin abinci a Nigeria - Save the Children

Save the Children ta ce akalla yara 200 za su iya rasa rayukansu a kullum saboda tsananin yunwa
Bayanan hoto,

Save the Children ta ce akalla yara 200 za su iya rasa rayukansu a kullum saboda tsananin yunwa

Kungiyar agaji ta Save the children ta ce matsalar karancin abinci mai gina jiki ta yi kamari a tsakanin yara 'yan kasa da shekaru biyar da ke yankin arewa-maso-gabashin Najeriya.

A wata sanarwar da kungiyar ta fitar, kungiyar ta kuma bayyana fargabar cewa akalla yara 200 za su iya rasa rayukansu a kullum saboda tsananin yunwa.

Kungiyar ta ce binciken da ta gudanar daga watan Yunin da ya gabata zuwa watan Oktobar da ya wuce, ya nuna cewa kimanin kashi 40 zuwa 50 cikin dari na yara 'yan kasa da shekarar biyar ne ke fuskantar matsanancin karancin abinci mai gina jiki a wasu sassan arewa maso gabashin Najeriya.

Kungiyar ta save the children ta dora alhakin halin da yaran ke ciki ne a kan matsalar tsaro da kuma karancin kayayyakin agaji.

Najeriya ta kwashe tsawon shekaru bakwai tana fama da rikicin Boko Haram, lamarin da ya janyo asarar dubban rayuka ya kuma daidaita miliyoyin mutanen yankin da gidajensu, inda suka zamo 'yan gudun hijira.